28 Satumba 2021 - 07:45
​Sojojin Yemen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Rumbun Makamai Na Sojojin Hadi

Sojojin kasar Yemen tare da taimakon sojojin sa kai na kasar sun kai farmaki da makamai masu linzami samfurin ballistic guda biyu kan rumbun ajiyar makamai na mayakan Abdurabbu Mansur Hadi a yankin Al-abdiyya cikin lardin Ma’rib.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shafin yanar gizo na Al-Khabarul Yemeni news ya na fadar haka. Ya kuma kara da cewa sojojin na Yemen sun yi amfani da makamai masu linzami kirar cikin gida don aiwatar da wadannan hare-hare, sannan akwai labaran da suka tabbatar da cewa an kashe wani babban kwamandan rundunar Hadi mai suna Abdullahi Sultan a wadannan hare-hari..

Kafin haka dai sojojin na Yemen sun kai irin wadannan hare-haren kan sojojin saudiya a lardin na Ma’arib.

342/